.
An haifi Sheikh Hamza a BicchiSheikh Hamza Rijiyar Lemu Kano, jihar Kano. a shekarar 1908.
Ya karɓi ilmi daga hannun wasu malamai a Kachna, Kano, kuma ya karɓi tariqar Tijjaniyya daga Sheikh Ahmad Tijjaniyya bin Usman, ya taso a ƙarƙashinsa, kuma sheikh dinsa, Sheikh Ahmad Tijjaniyya bin Usman, ya ba shi izini bada tariqar Tijjaniyya da gabatar da ita.
Kuma yana tare da sheikh dinsa Sheikh Ahmad Tijjani A lokacin da suka tarbi Sheikh Ibrahim inyass Al-Kaulakhi, a dawowarsa Najeriya karo na biyu.
Kuma ya sabunta karɓar tariqar a hannun Sheikh inyass ; Sheikh Ibrahim ya ba shi cikakken izini a tariqar Tijjaniyya.
Sheikh Hamza ya kasance mai kare tariqa, ba ya tsoron kakkausar magana saboda hakan, ya rubuta littattafai da wasiku kan tariqar, kuma Sheikh yana da ƙarfi da kuzari na musamman a duk motsuwarsa, yana da himma mai girma.
Kuma yana da mabiya da masoya a cikin Najeriya da wajen ta, musamman a Kano da Kachna, ya ba da izini kuma ya gabatar da mutane da yawa marasa ƙidaya; wasu daga cikinsu a birnin Kano kamar Sheikh Muhammad Yanbiu,
a Ghana kamar Sheikh Ahmad Tijjani (waala waali), a Burkina Faso kamar Sheikh Sulaiman Sore da Sheikh Yunus Yabu.
Kuma yana da majalisa ta musamman a gidansa inda yake gabatar da darussa ga musamman da jama’a, kuma bai daina yada ilmi tsakanin ɗalibansa har zuwa ƙarshe rayuwarsa.
Kuma Sheikh yana da makarantu masu yawa, waɗanda ‘ya’yansa da jikokinsa da wasu mabiya ke shugabanta a ƙasashe daban-daban.
Sheikh ya rasu a safiyar ranar Lahadi 1445/10/19, wadda ta dace da 2024/4/28, ya rasu yana da kimanin shekaru 116; Allah ya jiƙansa ya gafarta masa ya haɗa shi da Annabi Muhammad. S W W amin
Leave a Reply